Mr. Ma ya kara da cewa, a lokacin da ake fuskantar barazana iri iri da ayyukan ta'addanci ke haddasawa, ya kamata kasashen duniya su bi ma'auni iri daya, su kuma sa niyyar yakar ta'addanci ba tare da nuna sassauci, ko ma'aunai mabanbanta kan yaki da ta'addanci ba.
Bugu da kari, a lokacin da ake kokarin tinkarar ta'addanci, ya kamata a mutunta ikon mulkin kasar da abun ya shafa. Sannan ya kamata kowace kasa mai alaka ta sauke nauyin dake wuyanta, ta yi kokari matuka wajen yakar ta'addanci.
Kaza lika Mr. Ma ya ce, ya kamata a bi ruhi da ka'idojin kundin mulkin MDD, a taka rawar MDD da kwamitin sulhun MDD wajen tinkarar ta'addanci cikin hadin gwiwa.
A matsayin wata muhimmiyar mamba daga cikin kasashen dake kokarin yakar ta'addanci. A 'yan shekarun baya bayan nan, kasar Sin ta kara yin hadin gwiwa da MDD da kungiyar hada kai ta Shanghai wato SCO, ta bayar da muhimmiyar gudummawarta wajen tinkarar ta'addanci tsakanin kasa da kasa. Don haka kasar Sin tana son ci gaba da hada kan sauran kasashen duniya, wajen shawo kan barazanar ta'addanci, da kuma shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya. (Sanusi Chen)