in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban babban taron MDD ya jaddada muhimmancin kare aukuwar tashin hankali
2018-02-13 11:11:21 cri

Shugaban babban taron MDD Miroslav Lajcak ya jaddada muhimmancin kare aukuwar tashin hankali. Jami'in ya bayyana hakan ne jiya Litinin yayin da yake jawabi a zaman kwamitin kula da ayyukan wanzar da zaman lafiya na musamman na babban taron majalisar.

Ya ce, an kafa MDD ne domin kare rayukan jama'a daga yake-yake, don haka, akwai bukatar majalisar ta kara zage damtse waje ganin ta sauke nauyin dake kanta.

Sai dai kuma jami'in na MDD ya yi bayanin cewa, kara daukar matakan kare aukuwar tashin hankali ba wai yana nufin rage aiwatar da matakan kiyaye zaman lafiya ba ne. Yana mai cewa yadda ake daukar matakan hana aukuwar tashin hankali cikin hanzari a wasu lokutan, yana taimakawa wajen kaucewa tura sojoji. Koda yake tura sojojin kiyaye zaman lafiya a wuraren babu tashin hankali sosai, zai ba su damar tabbatar da zaman lafiya a lokacin da suke wuraren, maimakon daukar mataki bayan da tashin hankali ya barke.

Lajcak ya kara da cewa, bai kamata a raba batun hana aukuwar tashin hankali da tabbatar da zaman lafiya ba. Yana mai cewa, abin da MDD ta mayar da hankali a kai shi ne, ayyukan siyasa na musamman, tawagogin shiga tsakani ko kuma ofisoshin MDD. Sai dai wajibi ne batun hana aukuwar tashin hankali ya kasance aikin da MDD za ta fadada shi.

Haka kuma, jami'in na MDD ya bayyana cewa, a ko da yaushe ma'aikatan wanzar da zaman lafiya suna goyon bayan harkokin siyasa ko na shiga tsakani. Kuma suna da alaka ta musamman da jagororin kasashe. Suna kuma taimakawa wajen gano alamun barkewar tashin hankali. Saboda, hana aukuwar tashin hankali wani bangare ne na aikin majalisar game da tabbatar da zaman lafiya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China