in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar wakilan Sin dake MDD ta shirya liyafar murnar bikin bazara na shekarar 2018
2018-02-13 15:47:35 cri
Jiya da dare ne, tawagar zaunannun wakilan Sin dake MDD ta shirya liyafar murnar bikin bazara a mazauninta dake birnin New York na kasar Amurka, inda shugaban babban taron MDD karo na 72 Miroslav Lajcak, mataimakiyar babban sakataren MDD Amina J. Mohammed da sauran manyan jami'an MDD da jakadun kasashe fiye da 100 dake MDD ciki har da na kasashen Amurka, Rasha, Birtaniya da sauransu sun halarci liyafar.

A jawabinsa Jakadan Sin dake MDD Ma Zhaoxu ya yi nuni da cewa, shekarar da ta gabata muhimmiyar shekara ce ga kasar Sin da ma dukkan duniya. Taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 da aka kammala a shekarar da ta gabata ya bude sabon babi na raya kasa na zamani mai tsarin gurguzu a dukkan fannoni, kuma yawan GDPn kasar Sin ya zarce kudin Sin Yuan biliyan 80000 da sauransu. Kana kasar Sin ta yi alkawari cewa, ya zuwa shekarar 2020, za a kawar da mazauna kauyukan kasar Sin dake fama da talauci bisa ma'aunin kasar Sin na yanzu.

Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, Sin za ta ci gaba da daukar nauyin tabbatar da iko da matsayin MDD, da hada kai da sauran kasashen duniya a kokarin da ake na samar da kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China