in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Afirka ta kudu ya yi murabus
2018-02-15 12:00:06 cri

Shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma, ya yi murabus daga mukamin sa. Cikin wani jawabi da Mr. Zuma ya gabatar da yammacin jiya Laraba, ya ce bai kamata ya bari kawunan 'yan jam'iyyar su ta ANC su rarrabu saboda bukatar kan sa ba.

Zuma ya kara da cewa, duk da bai amince da dalilan jam'iyyar sa na tilasa masa sauka daga mulki ba, musamman cikin makwanni 2 da aka shafe ana fama da tirka tirkar siyasa a kasar, ya amince da ya sauka.

ANC dai ta shafe makwanni 2 tana matsawa Zuma lambar sauka daga karagar mulki. Daga bisani kuma mambobin kwamitin koli na musamman na jam'iyyar sun tattauna a ranar Litinin, inda suka yanke shawarar yiwa shugaban kiranye. Sai dai kuma jam'iyyar ta baiwa Mr. Zuma zuwa ranar Laraba da ya sauka da kan sa ko a tsige shi.

A jawabin sa na barin aiki, shugaba Zuma ya bayyana cewa, babu wani laifi da ya aikata illa dai kawai wasu jagororin jam'iyyar sa ta ANC ne ke neman ganin bayan sa.

Yanzu haka dai mataimakin shugaban kasar Cyril Ramaphosa ne ke rikon mukamin shugabancin kasar, inda ake fatan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a Alhamis din nan ko Jumma'a.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China