A jiya Talata ne jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta kudu ta tabbatar da cewa, za ta yiwa shugaba Jacob Zuma kiranye. Sakataren jam'iyyar ta ANC Ace Magashule shi ne ya shaidawa manema labarai hakan a birnin Johannesburg bayan ganawa da kwamitin zartarwas jam'iyyar a ranar Litinin da dare.
Ya ce, kwamitin zartaswar jam'iyyar ya yanke shawarar yiwa shugaba Zuma kiranye, zai kuma yiwa jagororin majalisar dokokin kasar bayani a yau Laraba game da wannan mataki.
Magashule ya ce jam'iyyar tana tattaunawa da Zuma kan yadda zai sauka daga mukaminsa cikin 'yan makonni. An kuma baiwa shugaba Zuma har zuwa yau Laraba domin ya mayar da martani game da matakin da jam'iyyar tasa ta dauka na yi masa kiranyen.
Sakataren na ANC ya ce, kwamitin zartaswar jam'iyyar ne ya yanke wannan shawara, kuma babu wanda zai canja shi. Sai dai ya ce, duk da wannan mataki da jam'iyyar ta dauka kan shugaba Zuma, jam'iyyar ANC za ta ci gaba da mutunta shi a matsayin daya daga cikin shugabanninta da suka ba da gudummawa a yaki da nuna wariyar launin fata a kasar.(Ibrahim)