in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani babban jami'in gwamnatin Nijeriya ya ce shugaban kasar zai sake tsayawa takara a shekarar 2019
2018-02-17 12:11:30 cri
Sakataren Gwamnatin Nijeriya Boss Mustapha, ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, shugaban kasar Muhammadu Buhari, zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar a shekarar 2019.

Da yake jawabi yayin wani gangami a Abuja, Boss Mustapha ya ce Muhammadu Buhari ya sauya yadda ake kallon shugabancin Nijeriya a ciki da wajen kasar.

Mustapha wanda shi ne babban jami'in gwamnati da yayi jawabi kan takarar Buhari a shekarar 2019, ya yi ikirarin cewa duk sauran masu neman tsayawa takarar ba su da wani abu da za su iya yi.

Shi dai Shugaba Buhari bai bayyana sha'awarsa ta tsayawa takarar ba a hukumance, sai da kungiyoyi da dama na ta bukatar ya sake tsayawa.

Cikin wata wasika da ya fitar a watan da ya gabata, tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo, ya shawarci shugaba Buhari da kada ya sake tsayawa takara.

Kuma tun daga wancan lokaci ne yake fafutukar kafa wata kungiya mai suna Coalition of Nigeria Movement da ake sa ran za ta koma jam'iyyar siyasa kafin lokacin zabe.

Nijeriya dai ta shirya gudanar da babban zabenta ne a watan Fabrerun 2019. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China