Wasu dalibai 22 da direban mota sun mutu a yayin da motar da suke ciki ta yi taho mu gama da wata babbar mota a lokacin da suka kan hanyarsu daga jihar Bauchi zuwa Kano a arewacin Najeriya, wani jami'i ya tabbatar da faruwar lamarin jiya Talata.
A cewar Kabir Ibrahim-Daura, kakakin hukumar kiyaye hadarurruka ta jihar Kano, akwai wasu mutane uku da suka samu munanan raunuka a lokacin hadarin.
Ya ce daga cikin daliban 22, guda 12 maza ne, sannan 10 mata ne.
Najeriya tana daga cikin kasashen duniya da aka fi samun yawaitar hasarar rayuka a sanadiyyar hadarurrukan mota, galibi an fi samun matsalar ne sakamakon rashin kiyaye dokokin tuki, da rashin kyawun titunan mota ko kuma na ababen hawan.(Ahmad Fagam)