Kwararru sun yi zargin rashin isassun matakan gudanarwa a kan iyakokin kasashen Afrika yana haifarwa kasashen yin hasarar kashi 5 cikin 100 na kudaden shigarsu.
James Kisaale, mataimakin kwamishinan hukumar tattara kudaden shiga na kasar Uganda (URA), ya fada haka a lokacin taron karawa juna sani da aka gudanar a Arusha game da sha'anin kasuwanci, ya bayyana cewa, ana hasarar makudan kudaden shiga a sakamakon rashin isassun manufofin gudanarwa a kan iyakokin wasu kasashen na Afrika, inda aka gano kashi 5 na kudaden shigarsu suna zurarewa.
Jami'in hukumar ta URA, ya buga misali da cewa, kungiyar hada kai da tabbatar da ci gaban tattalin arziki (OECD), ta yi wani nazari a shekarar 2013, inda ta gano cewa, faduwar farashin kayayyaki a duniya zai karu da kashi 1 cikin 100 wanda adadinsa zai zarta dala biliyan 40 na kudaden shiga, yayin da kasashe masu tasowa su ne za su fi cin gajiyarsa.
Kisaale ya bayyana a lokacin taron tattaunawa na wuni guda cewa, bangarorin da za su fi bayar da gudunmowa mafi tsoka a kasashen kudu da hamadar Saharar Afrika sun hada da fannonin fasahar kere kere da saukaka hanyoyin samar da takardun da suka shafi harkokin cinikayya.(Ahmad Fagam)