Gwamnatin Najeriya ta bayyana shirinta na yin ban kwana da kungiyoyin kasa da kasa kimanin 90 wadanda a baya take mu'amala da su, a wani mataki na kara yin tsimin kudi.
Ministan harkokin kudin kasar Kemi Adeosun wadda ta bayyana hakan, ta ce yanzu gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai yi nazarin kungiyoyin kasa da kasa da gwamnatin kasar ke mu'amala da su.
A cewar ministar, gwamnatin Najeriya na kashe kimanin dala milyan 70 a kan wadannan kungiyoyi a ko wace shekara, a saboda haka, yanzu Najeriyar za ta ci gaba da hulda da kungiyoyi 220 ne cikin 310. (Ibrahim)