in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CBN ya kara yawan kudaden musaya domin kare darajar Naira
2017-06-14 09:22:57 cri

Babban bankin tarayyar Najeriya CBN, ya zuba karin kudade da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 413.5 ga bankunan kasuwancin kasar, a wani mataki na kare darajar kudin kasar Naira, wadda a baya bayan nan ta fuskanci babbar karaya bisa sauran kudaden musayar waje.

Kakakin babban bankin kasar Isaac Okorafor ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata, yana mai cewa, CBN na da kwarin gwiwar ganin kudin kasar ya farfado, bisa farashin dalar Amurka, da ma sauran kudaden musayar waje da ake ta'ammali da su a kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China