in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin Afreximbank na neman dala miliyan 300 domin bunkasa masana'antu a Afirka
2017-09-08 09:07:03 cri

Bankin Afreximbank na neman zuba kudi da yawan su ya kai dala miliyan 300 a sassan raya masana'antu, da bunkasa ababen more rayuwa, domin bunkasa ci gaban nahiyar Afirka.

Da yake tabbatar da wannan kuduri, mataimakin shugaban bankin George Elombi, ya shaidawa 'yan jaridu a birnin Nairobi cewa, bankin na fatan tattara wadannan kudade ne da nufin kara yawan kudin da ake baiwa sassa masu zaman kan su a matsayin rance.

Ana dai fatan kudaden rancen, za su shiga fannin daga matsayin matsakaitan masana'antu, ta yadda Afirka za ta rage dogaro da kayayyakin da ake shigarwa daga ketaren ta. Kaza lika za a fadada kafuwar yankunan ciniki cikin 'yanci, da fannin samar da makamashi. Bayan ga karin kudaden haraji da gwamnatocin nahiyar za su rika samu karkashin manufar.

Mr. Elombi ya ce, dogaron da nahiyar Afirka ke yi da hajoji daga ketare, na haifar da matsi ga tattalin arzikin kasashen nahiyar, saboda hauhawar farashin irin wadannan hajoji. Ya ce, bunkasa irin wadannan masana'antu, na iya baiwa nahiyar damar samun karin guraben ayyukan yi.

Za dai a fara gudanar da tsarin na zuba jari ne daga kasar Mauritius, sai kuma Kenya, kafin kuma tsarin ya shiga Nigeria.

Tsarin dai zai karfafa hada hadar hannayen jari a nahiyar Afirka. Shi ne kuma karon farko da babban banki irin Afreximbank, zai samar da irin wannan dama ga daidaikun sassa na masu zuba jari.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China