Alkaluman hasashen tattalin arzikin kasar sun nuna cewa, an samu farfadowa daga komadar tattalin arzikin da kasar ta shiga a rukunin watanni uku na biyu na wannan shekara, kamar yadda gwamnan babban bankin Najeriyar CBN, Godwin Emefiele, ya shedawa 'yan jaridu a lokacin taron kwamitin tsara al'amurran kudin kasar MPC a Abuja, babban birnin kasar.
A cewar kwamitin, saukaka harkokin tafiyar da kudaden kasar MPR, zai iya bayyana kokarin kwamitin wajen samar da cigaba da samar da ayyukan yi ta hanyar karfafa matakan samar da rancen kudade wanda zai iya yin tasiri game da tattalin arziki na zahiri.