in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta ci gaba da dora muhimmanci ga batun samar da ayyukan yi yayin da ake yiwa tattalin arziki gyaran fuska
2018-02-16 12:25:28 cri

Hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin (NDRC) ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da dora muhimmanci ga batun samar ga guraben ayyukan yi, yayin da take kokarin yiwa tattalin arzikinta gyaran fuska.

Mai magana da yawun hukumar ta NDRC Meng Wei ita ce ta bayyana hakan, tana mai cewa, gwamnati ta dauki wannan mataki ne, ta yadda za a samar da ci gaba mai inganci a kasar a shekarar 2018 da muke ciki.

Ta ce, batun samar da guraben ayyukan yi a wannan shekara, batu ne mai muhimmancin gaske, yayin da ake saran kimanin dalibai miliyan 8.2 za su kammala karatu a kwalejoji daban-daban, baya ga mutane miliyan 9.7 marasa aikin yi da wasu dake zaman kashe wando da su ma ke bukatar ganin sun samu aikin yi.

Ta kuma bayyana cewa, kokarin da mahukuntan kasar Sin ke yi na neman ci gaban tattalin arziki, shi ne tabbatar da ganin an samar da guraben ayyukan yi ga al'ummar Suinawa. Ta ce a wannan shekara, kasar Sin za ta inganta karfin sabbin kamfanoni na samar da sabbin guraben ayyukan yi, da rage gibin dake tsakanin yankunan kasar, da inganta rayuwar mazauna yankunan karkara da bullo da managartan manufofi game da samar da guraben ayyukan yi.

Bugu da kari, gwamnati za ta kara yiwa manufofin da suka shafi ilimin sana'o'in hannun gyaran fuska, ta yadda za a rika horas da karin jami'ai da ragowar mutane sana'o'i na musamman. Za kuma a karfafawa 'yan ci rani gwiwar fara sabbin sana'o'i. A hannu guda kuma hukumar tana tattaunawa da bankunan dake tsara manufofi kan yadda za su agaza musu da kudaden aiwatar da irin wadannan manufofi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China