Mahukuntan kasar Sin sun sha alwashin shawo kan kalubalen ci gaba da kasar ke fuskanta a shekarar 2018 dake tafe, ciki hadda batun yaki da fatara, da yaki da gurbatar muhalli.
Wani sako dake kunshe cikin wasu takardun bayanai da mambobin kwamitin koli na sashen siyasar JKS suka fitar, bayan taron su na yau juma'a ya nuna cewa, akwai bukatar fitar da wasu dabaru, wadanda za su kunshi hanyoyin tunkarar manyan kalubale guda 3.
Sakon ya nuna cewa, ya zama wajibi kasar Sin ta sauya akalar sassan hada hadar kudade, ta yadda za su zamo suna ba da gudummawa ga ci gaban al'umma, a wani mataki na dakile aukuwar matsalolin da ake gujewa.
Game da yaki da fatara kuwa, sakon ya nuna bukatar tsagin mahukunta, ya tallafawa al'ummar kasar da karin karfin gwiwa, ta yadda za su fitar da kan su daga kangin talauci, su kuma kai ga samun ilimi mai fa'ida da suke bukata.
A fannin shawo kan gurbatar muhalli kuwa, an bayyana bukatar rage fitar da iska mai gurbata muhalli ta yadda muhalli zai inganta.
Takardun bayanan sun kuma bayyana cewa, Sin za ta ci gaba da bin manufar neman ci gaba mai dorewa cikin daidaito, a matsayin hanya ta aiwatar da manufofin bunkasuwar ta.(Saminu Alhassan)