Wannan sanarwa da aka fitar bayan kammala taron majalissar na ranar Laraba, wanda firaministan kasar Li Keqiang ya jagoranta, ta bayyana aniyar gwamnati( na karfafa matakan maye gurbin basussuka da kadarori, da aiwatar da sauye sauye a fannin mallakar hajoji, da na tsara managartan dabarun kasuwanci, da kuma kare fadawa mummunar hasara.
Sanarwar ta kara da cewa, kamfanoni mallakar gwamnati za su ci gaba da samun kulawa a fannin tabbatar da 'yancin su, karkashin tanaje tanaje na dokoki da kuma damar da kasuwanni ke samarwa.
Taron ya kuma amince da irin nasarorin da aka cimma a bara, duba da ci gaban da kamfanoni mallakar gwamnati suka samu a shekarar.
Kaza lika darajar kadarorin masana'antu idan an danganta da bashin su, ta daga musamman wadanda ke da jarin da ya haura Yuan miliyan 20, adadin da ya yi kasa da kaso 55.5 bisa dari a karshen shekarar ta bara, sabanin kaso 56.1 bisa dari da aka samu a shekarar da ta gabata. A bangaren masana'antun da gwamnati ke iko da su kuwa, adadin ya kai kaso 60.4 bisa dari.
An kuma tattauna game da matakan da za a ci gaba da dauka, game da warware matsalar bashi ta hanyar musaya da kadarori a fannin kamfanonin gwamnati. (Saminu)