Bayan shekaru kasar ta Sin na yunkurin hakan, wannan yarjejeniya za ta ba da damar shigar da tsarin, cinikayyar albarkatun mai cikin hajojin da ake hada-hadar hannayen jarin su, a kasuwar kasa da kasa ta makamashi ta Shanghai ko INE a takaice.
A cewar hukumar dake sanya ido kan harkokin da suka jibanci hada hadar hannayen jari ta Sin CSRC, yarjejeniyar za ta kuma baiwa Sin damar yin tasiri a fagen kayyade farashin danyen mai, baya ga tsarin kasa da kasa da ake da shi a yanzu.
Sin ce dai kasa ta biyu mafi amfani da albarkatun mai bayan Amurka, kuma bukatarta ga hajar na iya karuwa a nan gaba, yayin da kasar ke dada bukatar makamashi domin bunkasa tattalin arzikinta.
A daya hannun kuma wannan tsari zai baiwa kudin kasar wato Yuan karin karfi, bisa cinikayyar albarkatun danyen man da kasar ke yi da sauran kasashen duniya.
Yanzu haka dai ana kayyade farashin albarkatun mai ne da dalar Amurka, matakin dake barazana ga bukatar Sin ta makamashi da kuma tattalin arziki.
Wannan yarjejeniya za kuma ta baiwa Sin damar kara taka muhimmiyar rawa, ta fuskar cinikayya da sauran kasashen duniya masu arzikin mai. (Saminu Hassan)