Mr. Magashule ya bayyana hakan ne yayin wani taron 'yan jaridu da ya gudana a birnin Johannesburg, inda ya yi tsokaci game da taron kwamitin zartaswar jami'iyyar ANC. Ya ce kwamitin zartaswar jam'iyyar ya amince da jan hankalin shugaba Zuma da ya yi murabus, zai kuma yi wa walikan jam'iyyar dake majalissar dokokin kasar karin haske game da hakan a gobe Laraba. (Saminu Hassan)