in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta kudu za ta kaddamar da takardun kudi don tunawa da Mandela
2018-02-12 11:57:16 cri

Babban bankin kasar Afrika ta kudu (SARB) ya sanar cewa, zai samar da takardun kudin kasar wadanda za'a dinga tunawa da marigayi Nelson Mandela.

An haifi marigayi tsohon shugaban kasar Afrika ta kudun Nelson Mandela ne a ranar 18 ga watan Yulin shekarar 1918.

A wata sanarwa da babban bankin kasar ya fitar ya ce, za'a samar da takardun kudin kasar na rand 10, 20, 50, 100 da 200 a matsayin mataki na tunawa da haihuwar Mandela.

Gwamnan babban bankin na SARB, Lesetja Kganyago ya ce, Nelson Mandela ya kasance a matsayin wani muhimmin ginshiki na rayuwar al'ummar kasar Afrika ta kudu.(Ahamd Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China