Wata sanarwa daga ofishin mai tsawatarwa na jam'iyyar ta ANC ta ce, ko da yake wannan batu ne na cikin gidan jam'iyyar, amma ya zama dole ta nisanta kan ta daga rahotanni masu kunshe da yadda shugaban jam'iyyar Cyril Ramaphosa, ya bayyanawa shugabannin majalissar dokokin kasar cewa wai shugaba Zuma na shirin sauka daga mukamin sa a ranar Asabar.
Rahotanni dai sun rawaito Mr. Ramaphosa na cewa, shugaban kasar zai sauka daga mukamin sa, ba kuma zai samu wata kariya daga bincike ba.
A ranar Alhamis kafofin watsa labaran Afirka ta kudu sun rawaito Mr. Ramaphosa, na shaidawa shugabannin majalissar dokokin kasar cewa, batun cirewa shugaba Zuma rigar kariya ba abu ne da za a tattauna a kai ba.
Rahoton dai na zuwa ne bayan da a ranar Laraba Ramaphosa ya bukaci al'ummar kasar da su kara hakuri, yayin da ake ci gaba da tattauna muhimman batutuwa tare da shugaba Zuma. (Saminu)