An tabbatar da cewa, lamarin ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a daren ranar Laraba, lamarin da ya haifar da katsewar layukan wutar lantarki, inda aka samu mummunan daukewar wutar lantarki, lamarin da ya sa na'urar dake dauko ma'aikatan daga karkashin kasa ta kasa yin aiki.
A cewar kakakin kamfanin Sibanye-Stillwater da ke gudanar da wannan mahakar zinari, wannan wani yanayi ne da ba'a saba ganin irinsa ba. Sai dai yace a nazarci yadda lamarin ya faru domin daukar matakan da suka dace.
An rawaito cewa kamfanin yayi amfani da injinan samar da lantarki don ceto ma'aikatan. A cewar rahotannin farko da aka fitar, injinoyin dake aiki sun fuskanci tangardar manhajar na'ura mai kwakwalwa a lokacin da suke fadi-tashin ceto ma'aikatan.(Ahmad Fagam)