in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin a MDD ya bukaci kwamitin sulhu da ya mayar da hankali kan muhimman batutuwa
2018-02-07 19:43:22 cri

Wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD Ma Zhaoxu, ya bukaci kwamitin sulhun MDD da ya mayar da hankali kan batutuwa masu muhimmanci tare da tabbatar da cewa ya sauke nauyin dake kansa yadda ya kamata.

Ma ya bayyana hakan ne jiya Talata yayin zaman mahawara na bainar jama'a game da ayyukan kwamitin sulhun. Ya ce akwai bukatar kwamitin sulhun ya yi amfani da kudade da karfinsa wajen magance muhimman batutuwa da kuma na gaggawa da suka shafi zaman lafiya da tsaro a duniya. Kana ya kara nuna tasirinsa kan matakan da ya ke dauka.

Wakilin na kasar Sin ya ce, kasarsa tana dora muhimmanci kan yiwa kwamitin sulhun gyaran fuska, tana kuma goyon bayan a kara yin gyaran fuskan da suka dace, musamman wajen samun wakilci da bakin fada a ji na kasashen masu tasowa. Ta yadda za a kara karfi da ikon kwamitin sulhun.

Da ya juya ga yadda kwamitin sulhun ke yanke shawara kuwa, Ma ya ce akwai bukatar a kara tuntubar juna ta yadda za a cimma daidaito. Ya ce wajibi ne a tabbatar da cewa, dukkan mambobin kwamitin sulhun suna da isasshen lokaci na nazartar duk wata sanarwa da aka fitar game da daftarin kuduri da kuma daftarin shugaba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China