in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi Allah wadai da amfani da sinadarai masu guba a Syria tare da yin kiran daukar matakai
2018-02-07 11:02:53 cri
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da amfani da sanadarai masu guba a Syria, inda ya bukaci hadin kan kwamitin sulhun MDD wajen binciko wadanda ke da hannu don daukar matakan shari'a.

Mataimakin kakakin mista Guterres, Farhan Haq, ya fadawa manema labarai cewa, sun yi matukar kaduwa bisa samun rahoton da aka fitar kwanan nan, game da yin amfani da sinadarai masu guba a Syria, wanda ya hada da yankin Idlib. Sakatare janar din ya kuma yi Allah wadai da babbar murya game da yin amfani da irin wadannan muggan makamai wanda babu wata hujja ta shari'a da ta yarda a yi amfani da su.

Guterres, ya nanata yin kira na neman hadin kan kwamitin sulhun MDDr domin tabbatar da ganin cewa wadanda suke da alhakin amfani da sinadaran masu guba a Syriar an gano su da kuma daukar matakan da suka dace kansu, Haq ya danganta cikas din da aka samu a tsakanin mambobin kwamitin MDDr ne ya haddasa rusa tawagar gudanar da bincike mai zaman kanta kan lamarin, inda ka gano cewa dukkanin bangarorin gwamnatin Syria da 'yan kungiyar masu da'awar kafa daular musulunci ta IS sun yi amfani da sinadarai masu gubar a Syria. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China