Hukumar ta bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labaru, tana mai cewa, a ranar 2 ga wannan wata, wani jirgin ruwa mai dauke da mutane fiye da 140 da ya nufi ratsa Bahar Rum zuwa Turai ya kife, inda mutane 27 kawai aka ceto bayan hadarin. Baya ga haka, wani jirnin ruwa na daban mai dauke da mutane kimanin 130 shi ma ya kife jim kadan bayan da ya bar gabar tekun Libya, an ce mutane 2 ne kadai aka ceto da ransu.
Bisa kididdigar da hukumar ta yi a cikin wannan shekarar, yawan bakin haure da 'yan gudun hijira da suka rasa rayukansu sakamakon hadarin jiragen ruwa a Bahar Rum ya wuce 4200, wanda ya zarta na shekarar da ta gabata wato 3770. (Bilkisu)