Yanzu haka dai hukumomi na ci gaba da tattara alkaluman wadanda hadarin ya rutsa da su.
Wani jami'in lafiya a birnin ya bayyanawa majiyar mu cewa, an garzaya da wasu daga majinyatan zuwa asibitoci masu zaman kan su dake sassa daban daban na birnin Uyo. Kaza lika ya bayyana cewa 'yan sanda da sauran jami'an tsaro basu bayyana takamaiman adadin wadanda wannan lamari ya shafa ba.
A daya hannun kuma, wani jami'in rundunar 'yan sandan jihar ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, gwamnan jihar Udom Emmanuel na cikin wadanda suka tsira ba tare da samun wani rauni ba yayin da ginin ya fadi, sai dai kuma jama'a da dama sun rasu baya ga wasu da suka jikkata.
Gwamnatin jihar Akwa Ibom dai ta ayyana Lahadi da Litinin din nan a matsayin ranekun zaman makoki, domin jimamin aukuwar wannan lamari. Har ila yau gwamna Udom Emmanuel ya bada umarnin cafke dan kwangilar dake ginin cocin da ta rubza, a wani mataki na tantance musabbabin aukuwar hadarin.(Saminu Alhassan)