Kungiyar tarayyar Afrika (AU), ta bayyana juyayi da kuma ta'aziyya ga al'ummar jamhuriyar Kamaru game hadarin jirgin kasan da ya faru a Juma'ar da ta gabata.
A sanarwar da AU ta fitar, Nkosazana Dlamini Zuma, shugabar kungiyar ta AU ta aike da sakon ta'aziyyar ga gwamnati da al'ummar kasar ta Kamaru, musamman ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su.
Mummunan hadarin ya faru ne a garin Eseka, a lokacin da jirgin kasan yake kan hanyarsa daga babban birnin kasar Yaounde zuwa birnin Douala.
Hadarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 80, sannan wasu fasinjoji 600 suka samu raunuka.
Gwamnatin jamhuriyar Kamaru ta ayyana Litinin a matsayin ranar hutu a duk fadin kasar, domin makoki ga wadanda suka rasu, sannan ta yi alkawarin tallafawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su.(Ahmad Fagam)