in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 9 sun rasu sakamakon wani hadarin mota a Uganda
2017-06-26 13:10:43 cri

Rahotanni daga yankin Mpigi dake tsakiyar kasar Uganda, na cewa mutane 9 sun rasa rayukan su, yayin da wasu 13 suka ji munanan raunuka, sakamakon wani hadarin mota da ya rutsa da su a jiya Lahadi.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan yankin Katonga Philip Mukasa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, mutane 6 da suka rasu yayin hadarin, na cikin wata karamar mota ne, yayin da sauran 3 ke cikin wata Taxi, kuma motocin biyu sun yi taho mu gama ne a babban titin Kampala zuwa Masaka.

Mr. Philip ya ce, an yiwa karamar motar kazamin lodi, inda mutane 8 ke cinkushe a cikin ta, maimakon mutane 5 da doka ta tanada, kuma motar ta yi watsi da wasu daga cikin fasinjojin dake cikin ta yayin aukuwar karon. Ya kuma bayyana karya dokokin hanya, da gudun wuce sa'a, a matsayin musabbanin aukuwar hadarin.

Shi ma wani mai magana da yawun 'yan sandan kasar Assan Kasingye, ya ce hadarin da ya auku da yammaci ya haddasa cunkoson ababen hawa na kusan sa'a guda, yayin da jami'ai ke ta kokarin kawar da tarkacen motocin da suka tare hanya. A hannu guda kuma an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin Buwamba, da na Masaka, domin samun kulawar jami'an lafiya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China