Rundunar sojin tace, Abubakar Shekau, shugaban Boko Haram, a halin yanzu yana sanya hijabai masu launin baki da shudi domin kaucewa fadawa komar dakarun Najeriyar.
A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar tace, Shekau yana kokarin tsira da rayuwarsa ne. Yana matukar kokarin tserewa farmakin da sojojin ke kaddamarwa kan kungiyar, inda ya dauki matakin sanya hijabi don yin shigar bultu a matsayin mace.
Sanarwar ta kara da cewa, an yiwa Shekau kallo na karshe ne sanye da bakin hijabi, sai dai a cewar rundunar sojojin dakarun Najeriya suna cigaba da kokari don farautar shugaban kungiyar 'yan ta'addan.(Ahmad Fagam)