in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Nijeriya sun ceto daya daga cikin 'yan matan Chibok
2018-01-05 09:53:45 cri
Dakarun dake yaki da kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Nijeriya, sun ceto wata daga cikin 'yan matan Chibok 276 da kungiyar ta sace a watan Afrilun 2014.

An ceto yarinyar mai suna Salomi Pugo ne da safiyar jiya Alhamis a wani daji dake kusa da garin Pulka mai nisan kilomita 165 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Kakakin rundunar sojin Onyeama Nwachukwu, ya ce bayanan Salami Pugo sun yi daidai da na mai lamba 86, cikin jerin 'yan matan Chibok dake hannun kungiyar Boko Haram.

A cewarsa, an ceto Salomi ne tare da wata Jamila Adams mai shekaru 14 da kuma yaro karami, inda ya ce dukkansu 3 na hannun rundunar sojin a jihar Borno, inda kuma ake duba lafiyarsu.

A ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne mayakan Boko Haram suka sace jimilar 'yan mata 276 na sakandaren 'yan mata ta Gwamnati dake garin Chibok na jihar Borno, a lokacin da suke rubuta jarabawar kammala karatu, inda 57 daga cikinsu suka tsare suka bar 219.

A kuma ranar 13 ga watan Oktoban 2016 ne aka saki wasu 21 bayan kungiyar ta cimma yarjejniya da Gwamnatin Nijeriya.

Ko a watan Mayun da ya gabata, kungiyar ta saki karin wasu 'yan matan 82 bayan wata yarjejeniyar.

Baki daya dai 'yan mata 106 ne Gwamnatin tarayya ta ajiye a cibiyarta na gyaran hali dake Abuja babban birnin kasar, kana a watan Satumban da ya gabata ta mayar da su makaranta, inda suka fara da karatun share fagen shiga Jami'a da Gwmanati ta tsara musammam saboda su a wata Jami'ar jihar Adamawa dake yankin arewa maso gabashin kasar. (Fa'iza Musatpha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China