Kamfanin dillancin labaran kasar ta Jordan Petra ya kuma ruwaito ministan na cewa, yadda kungiyoyin 'yan ta'adda ke kai hari kan masu Ibada da fararen hula, ya nuna munin akidunsu. A don haka ya ce, akwai bukatar a kara hada kai da daukar matakai don ganin bayan ayyukan ta'addanci. Ya kara da cewa, kasarsa tana goyon bayan matakan da mahukuntan Najeriyar ke dauka na yaki da 'yan ta'adda.
Wani matashi ne dai ya kutsa kai cikin wani masallaci a lokacin sallar Asubahin ranar Laraba, sannan ya tayar da abubuwan fashewar dake jikinsa. Baki daya dai mutane 10 ne aka tabbatar sun gamu da ajalinsu sanadiyyar harin, ciki har da mahaifin maharin. (Ibrahim)