in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin Boko Haram ya hallaka mutane 5 a arewa maso gabashin Najeriya
2018-01-20 12:54:14 cri

Mahukunta a Najeriya sun ce a kalla mutane 5 ne suka mutu a wani harin da ake zargin mayakan Boko Haram da kaddamarwa a kauyen Kaya dake jihar Adamawa a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Yusuf Muhammed, shugaban karamar hukumar Madagali, wanda ya tabbatar da mutuwar mutanen biyar, ya ce an kaddamar da harin ne da misalin karfe 10 na yammacin ranar Alhamis.

Ya ce mutane da dama ne suka jikkata a sanadiyyar harin, kana an lalata gidaje da barnata dukiyoyi masu yawa a sanadiyyar harin.

Shugaban karamar hukumar ya ce, sakamakon yawaitar hare-hare a garuruwan dake yankin mutane da dama sun kauracewa gidajensu, inda suka kaura zuwa wasu jihohin dake makwabtaka da jamhuriyar Kamaru.

Shugaban ya kara da cewa, an kashe wasu mutane 3 a wani harin na daban a kauyen Pallama a ranar Talata, inda ya ce an samu hasarar rayuka kimanin 10 a yankunan, a sanadiyyar munanan hare-haren da aka kaddamar daga ranar 1 ga watan nan na Janairun shekarar 2018.

Othman Abubakar, mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar, shi ma ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya kara da cewa, hukumar 'yan sandan ta fara tattara bayanai game da al'amarin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China