in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Boko Haram sun halaka mutane uku a Kamaru
2018-01-11 19:13:34 cri
Rahotanni daga Kamaru na cewa, wasu da ake zaton mayakan Boko Haram ne sun halaka a kalla mutane 3 a wani hari da suka kaddamar ranar Laraba da dare a yankin arewa mai nisa na kasar.

Harin dai ya faru ne a yankin Kolofata dake arewacin kasar mai iyaka da Najeriya. Ana zaton mayakan sun kai harin ne a kokarin da suke na kwace kayan abinci daga mazauna wurin, yayin da kayan abincinsu ke shirin karewa.

Wani basarake a yankin Kolofata wanda ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce ya kamata jama'a su kasance cikin shirin aukuwar hare-haren mayakan daga lokaci zuwa lokaci, ganin yadda tun watanni da suka gabata mayakan na Boko Haram ke fama da karancin abinci.

Har ila a daren ranar Laraban, mayakan na Boko Haram sun mamaye wasu kauyuka dake kusa da yankin Mayo Moskota, inda suka tilastawa kauyawan arcewa garin Nguetchewa, da aka tura dakarun gwamnatin Kamaru.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China