Mai magana da yawun sojojin Najeriya ya tabbatar da cewa sama da mayakan Boko Haram 107 ne dakarun Najeriyar suka hallaka a yakin da suke yi da 'yan ta'addan.
Kakakin rundunar sojin Sani Kukasheka Usman, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, an kafa wata runduna ta musamman ta "Deep Punch 2", wanda ke aikin bankado dukkan maboyar mayakan 'yan ta'addan a arewa maso gabashin kasar.
A cewarsa, a ranar Litinin an kashe mayakan Boko Haram sama da 50 a yankunan gabar tafkin Chadi, a kusa da jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, inda aka kama tare da lalata makamai da alburusai masu yawa na mayakan kungiyar.
A cikin wannan ranar, an hallaka wasu mayakan na Boko Haram 57, a lokacin da sojojin ke gudanar da aiki a yankin Metele na jihar Borno.
Ya ce, motar mayakan na kungiyar ta Boko Haram ta hallaka sojojin Najeriyar 4 da wani ma'aikacin sa-kai guda.
Dakarun Najeriyar sun samu gagarumar galaba a yakin da suke da mayakan Boko Haram, inda dakarun suka fatattaki mayakan daga babban sansaninsu dake dajin Sambisa.(Ahmad Fagam)