Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarun ta sun ceto wasu mutane su 85 dake tsare a hannun mayakan Boko Haram. Rundunar ta ce an ceto mutanen ne da yammacin ranar Talata yayin wani samame na hadin gwiwa da sojojin suka gudanar a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.
Da yake karin haske game da hakan, kakakin rundunar Sani Usman, ya ce mutanen sun samu kubuta ne bayan da sojojin suka yiwa wata maboyar 'ya'yan kungiyar dake yankin karamar hukumar Ngala dirar mikiya. Kana sojojin sun hallaka dakarun kungiyar 11.
Har ila yau sojojin sun lalata maboyar mayakai, da kayayyakin da suke amfani da su wajen kaddamar da hare hare, da kuma wuraren sarrafa kayan yaki da suke da shi a wurin.
Bugu da kari sojojin sun kwace wata mota da dakarun na Boko Haram ke amfani da ita mai dauke da babbar bindigar yaki, da wasu rigunan daura ababen fashewa, da wasu ababen fashewa masu yawa. Baya ga sauran makamai da harsasai da dama da sojojin suna gano.(Saminu Alhassan)