A ranar Litinin gwamnatin Najeriya ta ankarar da manyan jami'an sojin kasar 70 cewar su zauna cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon fantsamar da mayakan Boko Haram suka yi zuwa wasu sassan kasar.
Babban hafsan sojojin Najeriyar laftanal kanal Tukur Buratai, ya sanar da cewa a halin yanzu mayakan 'yan tada kayar baya suna cikin tsaka mai wuya, kuma a yanzu sun fi mayar da hankali ne wajen kaddamar da hare hare a wasu kananan wurare da wuraren da ba su da wadataccen tsaro, kuma suna kokarin yin kaura zuwa wasu yankuna da za su iya samun mafaka a sassan kasar.
Buratai ya bada tabbacin cewa, sojojin kasar za su kakkabe dukkan sauran maboyar 'yan ta'adda a kasar, ya kara da cewa rundunar sojin Najeriyar a shirye take a ko da yaushe ta gudanar da ayyukanta na wanzar da tsaron kasar.
Domin tabbatar da wannan shiri, babban hafsan sojin kasar ya bada tabbacin cewa, hukumar gudanarwar sojin Najeriyar za ta yi dukkan abin da ya dace wajen samar da muhimman kayayyakin aiki da sojojin kasar ke bukata domin magance kalubalolin tsaro a kasar kamar yadda doka ta tanada.(Ahmad Fagam)