Da yake bayyana gamsuwa da hakan, shugaban hukumar zartaswar kungiyar Moussa Faki Mahamat, ya jinjinawa masu ruwa da tsaki game da cimma nasarar hakan.
Yarjejeniyar dai ta kunshi dakatar da kiyayya da juna, da kare rayukan fararen hula, tare da bada damar gabatar da kayayyakin jin kai ga masu bukata. An kuma sanya hannu kan ta ne yayin taron kungiyar raya gabashin Afirka ta IGAD, wanda aka bude a ranar 17 ga watan nan a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.