Mr. Geng Shuang ya fadi haka ne a lokacin da yake bayyana ra'ayinsa game da sabbin ra'ayoyin da bangarorin da abin ya shafa suka bayar, game da sabon halin da ake ciki a yankin Koriya.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, ma'aikatar kula da harkokin dinkuwar Koriya ta kudu ta bayyana cewa, a nan gaba, bangaren Koriya ta kudu za ta fi mai da hankali kan lallashin kasashen Koriya ta arewa da Amurka da su tattaunawa tsakaninsu.
A waje daya, mataimakin sakatare mai kula da harkokin wajen kasar Amurka Mr. Mike Pence, ya kuma bayyana cewa, kasashen Amurka da Koriya ta kudu sun cimma matsaya daya kan batun nukiliyar Koriya ta arewa, wato daga farko bangaren Koriya ta kudu zai soma yin mu'amala da tattaunawa da bangaren Koriya ta arewa, sannan mai yiyuwa ne kasashen Amurka da Koriya ta arewa za su yi mu'amala da tattaunawa tsakaninsu kai tsaye a nan gaba. (Sanusi Chen)