in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bukaci Japan da ta himmatu wajen inganta dangantaka dake tsakaninsu
2018-01-23 20:19:31 cri
Kasar Sin ta bukaci Japan da ta martaba kudurinta wajen ganin ta inganta alakar dake tsakaninta da kasar Sin, ta kuma nuna hakan a zahiri ta managartan manufofi da kuma a aikace.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying ce ta bayyana hakan a yau Talata yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a nan birnin Beijing, bayan da firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya jaddada kudurin kasarsa na bunkasa dangantaka da kasar Sin.

Baya ga kalaman da Aben ya yi cikin jawabin da ya gabatar dangane da manufofinsa yayin taron abinci mai gina jiki na wannan shekara a ranar Litinin, shi ma ministan harkokin wajen kasar ta Japan Taro Kono ya ce Japan za ta yi amfani da bikin cika shekaru 40 da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da kawance tsakanin kasashen biyu a matsayin wata dama ta bunkasa musaya tsakanin al'ummomin kasashen biyu da kuma karfafa hadin gwiwar tattalin arziki tsakaninsu

Madam Hua ta ce, kasar Sin tana fatan Japan za ta hada kai da kasar Sin wajen kara yin shawarwari da amincewa da juna, kana su daidaita bambance-bambancen dake tsakaninsu yadda ya kamata domin daga matsayin dangantakar dake tsakaninsu zuwa matakin da ya dace. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China