Rahotanni na cewa, a jiya ne shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya ce, a shirye kasarsa take ta tattauna da Koriya ta Kudu, game da yiwuwar kasar ta halartar gasar ta Olympics da za ta gudana a birnin PyeongChang na kasar Koriya ta Kudu a shekarar 2018.
Shi ma shugaba Moon Jae-in na Koriya ta Kudu ya yi maraba da jawabin da takwaransa na Koriya ta Arewa ya yi a murnar sabuwar shekara, inda ya umarci jami'an gwamnatinsa da su dawo tattaunawa tsakanin Koriyoyin biyu, kana su zana matakan da suka dace a dauka na ganin Koriya ta Arewar ta shiga gasar. (Ibrahim Yaya)