in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi da Jacob Zuma sun taya juna murnar cikar kasashen su shekaru 20 da kulla huldar diflomasiyya
2018-01-01 17:01:15 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Afirka ta kudu Jacob Zuma, sun taya juna murnar cikar kasashensu shekaru 20 da kulla huldar diflomasiyya.

Da yake gabatar da sakon taya murnar kasarsa ga shugaba Zuma, shugaban Xi ya ce yana fatan ci gaba da aiki tare da jagoran na Afirka ta kudu, domin kara gina alakar Sin da Afirka ta kudun, ta yadda hakan zai ba da damar cin gajiya ga al'ummun sassan biyu.

Ya ce Sin ta amince da karbar bakuncin taron kolin FOCAC nan gaba cikin wannan sabuwar shekara ta 2018, bisa shawarar shugaba Zuma, da ma bukatun sauran kasashen Afirka. Kaza lika shugaba Xi ya bayyana fatansa na ci gaba da cudanya da shugaba Zuma, da sauran shugabannin kasashen nahiyar, don ganin an cimma nasarar gudanar da taron koli na bana. Ya ce fatan dai shi ne taron ya bunkasa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da sauran kasashen Afirka.

A nasa bangaren, shugaba Zuma cewa ya yi kasar Sin da Afirka ta kudu, sun dade suna hadin gwiwa a fannonin da suke shafar moriyar su, suna kuma hada kai wajen fuskantar sabbin kalubale, da barazana dake fuskantar duniya. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China