A ranar Larabar nan ne dai Koriya ta Arewa ta bude kafar shiga zirin Panmunjom wanda ya dade a rufe. Ana sa ran wannan kafa za ta bada dama ga kasashen makwaftan juna, su zanta game da tawagar Koriya ta Arewa da ake fatan za ta halarci gasar wasannin lokacin hunturu da za a yi a birnin PyeongChang na Koriya ta kudu.
Makatin ya zo ne kwana guda, bayan da Koriya ta kudu ta bayyana shawarar gudanar da taron manyan jami'ai na kasa da kasa, domin tattauna batun samarwa tawagar jami'an damar zuwa Koriya ta kudu, taron da zai gudana a ranar 9 ga watan nan.
Game da hakan, Mr. Geng ya ce Sin na goyon bayan inganta dangantakar sassan biyu, da kaucewa ruwa wutar rikici, da raba zirin Koriya da makaman nukiliya. Har ila yau Sin na fatan sassan biyu za su yi amfani da wannan dama wajen cimma buri daya da zai amfane su. (Saminu Hassan)