in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar MDD ta yabawa kokarin gwamnatin kasar Sin na rage iska mai gurbata muhalli
2017-12-03 12:44:33 cri

Wata jami'ar sashen kare muhalli ta MDD ta yabawa kokarin gwamnatin kasar Sin na rage yawan iska mai gurbata muhalli a Beijing, babban birnin kasar.

Helena Valdes, wata kwararriyar ce a fannin samar da dauwamamman cigaba da sauyin yanayi wacce ke aiki da shirin kare muhalli na MDD, ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi cewa, kasar Sin ta nuna jajurcewa da yin aiki tukuru wajen magance matsalar iska mai gurbata yanayi.

Valdes ta ce, a lokacin da kasar Sin ta yi bincike ta hanyar kimiyya inda ta gano yawan iskar dake gurbata muhalli a Beijing, babban birnin kasar, kasar ta bullo da wani shiri na magance yawaitar iskar dake gurbata muhalli a birnin.

Ta ce a halin yanzu hukumar lafiya ta duniya WHO tana bibiyar ingancin iska a wasu manyan birane na duniya ciki har da birnin Beijing, WHO ta gano cewa ana samun gagarumin cigaba wajen rage adadin iskar dake gurbata muhalli a birnin.

Ta ce gwamnatin kasar Sin ta fidda wasu manyan masana'antu daga birnin Beijing, kana tana kokarin karfafa gwiwa ga mazauna birnin wajen yin amfani da makamashi mai tsabta.

Valdes, wadda ke jagorantar hukumar kula da sauyin yanayi da samar da iska mai tsabta (CCAC), ta ce ya kamata kasashen Afrika su koyi darasi daga irin nasarorin da kasar Sin ta samu.(Ahamd)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China