in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco ta yi Allah wadai da harin ta'addanci a masallaci a Najeriya
2017-11-23 09:52:25 cri
A wani labarin kuma, sarki Mohammed VI na kasar Morocco ya yi Allah wadai da babbar murya na harin ta'addancin da aka kaddamar kan wani masallaci a garin Mubi dake Najeriya.

A sakon da ya aikewa shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar, sarkin na Morocco yayi tur da wannan mummunan aiki na bata gari kuma matsorata, wanda ya ci karo da koyarwa addinin Islama kuma ya saba da hakkin dan adam.

Kana ya jaddada cikakken goyon bayansa ga a'lummar Najeriya a wannan yanayi na bakin ciki.

Sarkin ya yi wa shugaba Buhari ta'aziyya da kuma iyalai da dangin wadanda harin ya rutsa da su.

Haka zalika sarkin na Morocco ya yi addu'ar samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka samu raunuka, tare da yin fata ga iyalan wadanda suka mutu na hakurin jure rashin da aka samu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China