Kamfanin dillancin labarai na MAP ya ruwaito cewa, an yanke shawarar ne yayin taron kwamitin zartaswar kungiyar da ya gudana ranar Asabar da ta gabata a garin Grand Bassam na kasar Cote d'Ivoire.
Shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomin Morocco Mohammed Boudra, ya ce za a gudanar da taron a Morocco ne la'akari da kokarinta na tabbatar da daidaito tsakanin birane da kuma yankuna.
An shirya gudanar da taron a Morocco ne bayan birnin Brazzaville na kasar Congo, ya janye daga karbar bakuncinsa, saboda matsalolin kudi da kasar ke fuskanta a halin yanzu.
UCLG Africa, kungiyace ta hadin kai da wakilan kananan hukumomin Afrika, wadda ta kunshi kungiyoyi 40 na kanana hukumomi na kasa daga dukkan sassan Afrika da kuma birane 2000 dake da mazauna sama da 100,000. (Fa'iza Mustapha)