in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana zargin tawagar MDD dake DRC da laifin yin lalata
2018-02-13 11:04:48 cri

Tawagar MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar demokuradiyar Congo(DRC) ta karbi rahotannin wasu zarge-zargen aikata ba daidai ba, ciki har da wasu laifukan yin lalata guda uku da ake zargin ma'aikatan nata da aikatawa.

Kakakin MDD Stephane Dujjaric shi ne ya bayyana hakan a jiya Litinin, yana mai cewa wadannan zarge-zarge sun shafi sojojin kasar Afirka ta kudu dake aikin wanzar da zaman lafiya.

Dujarric ya ce, zarge-zargen yin lalata guda ukun da aka gabatarwa majalisar sun shafi wasu baligai ne. Kuma ana zargin cewa, lamarin sun faru ne a garuruwan Sake, da Beni, da Goma dake arewacin lardin Kivu.

Ya ce, yanzu haka asusun kula da yawan jama'a na MDD yana kokarin tabbatar da cewa, an taimakawa wadanda aka ci zarafin nasu ba tare da bata lokaci ba.

Kakakin ya ce, zargi na hudu ya shafi wani yaro dan shakara 17 ne da sojojin kiyaye zaman lafiya suka ci zarafinsa a gabashin lardin Kasai. Yanzu haka dai an mika yaron hannun asusun tallafawa kananan yara na MDD domin samun kulawar gaggawa yayin da a hannu guda, ofishin hadin gwiwa na MDD dake kare hakkin bil-Adama ke kare lafiyarsa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China