Wata sanarwar hadin gwiwa da kungiyar tarayyar Afirka, da MDD, da kungiyar tarayyar Turai(EU) da kuma kungiyar kasashen dake magana da harshen Faransanci(IOF) suka sanyawa hannu, sun bayyana cewa, makonni shida tun bayan amincewa da tanade-tanaden gwamnatin wucin gadi, wadda daga bisani za a gudanar da karbabben zabe a watan Disamban shekarar 2017, har yanzu bangarorin da abin ya shafa ba su kammala tattaunawa game da matakan aiwatar da wannan yarjejeniya ba. Kuma hakan na iya mayar da hannun agogo baya.
Kungiyoyin sun kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a kasar, ciki har da magoya bayan shugaban kasa da bangaren 'yan adawa da su kara himma, don ganin an kammala wannan tattaunawa.
Haka kuma.kungiyoyin sun bukaci dukkan bangarorin kasar, da su goyi bayan yunkurin shiga tsakanin da taron CENCO ke jagoranta, tare da tabbatar da ganin an aiwatar da yarjejeniyar ranar 31 ga watan Disambar da aka sanyawa hannu. Matakin da zai kai ga gudanar karbabben zabe a kasar.(Ibrahim)