in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani hari ya yi sanadin mutuwar dakarun MDD 14 da na Gwamnatin DR Congo 5
2017-12-09 12:29:02 cri

Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake aiki a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo wato MONUSCO, ya ce a kalla dakarunsa 15 ne suka mutu yayin wani hari da ake zargin 'yan tawayen ADF da suka kai wa yankin gabashin kasar.

Wata sanarwa da shirin ya fitar, ta ce harin da aka kai arewacin lardin Kivu, ya kuma yi sanadin mutuwar dakarun Gwamnatin kasar 5 tare da raunata dakarun MONUSCO 53.

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterress ya soki harin da kakkausar murya yana mai bayyana shi a matsayin hari mafi muni da aka kai wa jami'an wanzar da zaman lafiya a baya-bayan nan.

Ya kuma kara da cewa, ba za a taba amincewa da irin wannan hari da aka kai wa dakarun majalisar da gayya ba, yana mai cewa ya yi daidai da laifin yaki.

A nasu bangaren, Mambobin kwamitin sulhu na majalisar, sun yi kira ga Gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da ta tabbatar da wadanda ke da hannu sun fuskanci shari'a.

Har ila yau, mambobin majalisar sun bukaci dukkan kungiyoyi masu dauke da makamai, su kauracewa ta da tarzoma. Sannan, sun karrama sojojin da suka sadaukar da rayukansu wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron fareren hula.

Bugu da kari, sun kuma jaddada goyon bayansu ga shirin wanzar da zaman lafiya na MONUSCO, wanda kuma shi ne shirin wanzar da zaman lafiya mafi girma na MDD. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China