in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF: Yara da ke fama da karancin abinci mai gina jiki 400,000 na cikin hadari a DRC
2017-12-13 09:41:20 cri
Asusun yara na MDD UNICEF, ya yi gargadin cewa a kalla yara kanana 400,000 a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo na iya rasa rayukan su, sakamakon karancin abinci mai gina jiki a shekarar 2018 mai zuwa.

Cikin wata sanarwa da asusun na UNICEF ya rabawa manema labarai, an bayyana yankin Kasai a matsayin wanda ya fi fuskantar wannan matsala, sakamakon tashe tashen hankula dake wakana a yankin, da yawan masu kaura, da raguwar amfanin gona da aka fuskanta cikin watanni sama da 18 a yankin.

Sanarwar ta ce duk da matsalar tsaro ta ragu, kuma wasu da suka tserewa gidajen su sun fara komawa, har yanzu ana cikin damuwa game da yanayin jin kai a wannan yanki.

Tashe tashen hankula dai sun haifar da karancin abinci, duba da cewa kaso 2 bisa 3 na mazauna yankin ba sa iya noma gonakin su, wanda hakan ya sabbabawa mutane miliyan 1.4 rabuwa da matsugunnan su.

A daya bangaren kuma, batun kiwon lafiya shi ma na fuskantar kalubale, inda ake fuskantar tarin matsaloli a duk lokacin da bukatar kaiwa al'ummun dake cikin bukatar tallafin kula da lafiya ta bijiro.

Alkaluman kididdiga dai sun nuna cewa, sama da yara kanana dake yankin na Kasai 750,000 ne ba sa samun isasshen abinci mai gina jiki, yayin da kuma cibiyoyin kula da lafiya na yankin 25 ke fuskantar karancin kayan inganta lafiyar jiki da ake bukata.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China