Bisa ga alkaluman, a mafi karanci iyalai kusan 50 ne rikicin ke tilasta musu kauracewa gidajensu a cikin ko wace sa'a guda a tsawon shekarar ta 2017, kamar yadda Farhan Haq, ya bayyana cikin rahoton da ofishin kula da al'amuran jin kai na MDDr ya fitar.
Haq ya ce, a halin yanzu yawan mutanen dake zaune a sansanonin 'yan gudun hijira a kasar ya tasamma miliyan 4 da dubu 49, kuma sama da kashi 60 bisa 100 na adadin mutanen kananan yara ne. Wannan shi ne adadi mafi yawa na mutanen da rikici ya tilasatawa ficewa daga mutsugunansu a Afirka baki daya.
A shekarar nan ta 2018, ana bukatar dala biliyan 1.68 don samar da agaji ga mutanen na DRC, amma har ya zuwa yanzu, kashi 3 bisa 100 kawai na kudaden da ake bukata aka tattara.
Rashin tsarin gwamnati mai inganci, da matsalolin hare haren kungiyoyi masu dauke da makamai, da yawaitar take hakkin bil Adama a kasar, kana da samun jinkirin wajen gudanar da manyan zabukan kasar sun haifar da matsanancin talauci a tsakanin al'ummar DRC.(Ahmad Fagam)