in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta ayyana cigaba da huldar cinikayya a kan iyakarta da Sudan ta kudu
2018-02-13 10:45:48 cri

A ranar Litinin Sudan ta sanar a hukumance cewa za ta cigaba da yin huldar cinikayya a kan iyakarta da makwabciyarta Sudan ta kudu, bayan samun umarni daga shugaban kasar ta Sudan Omar al-Bashir, kamar yadda jaridar Tribune ta Sudan din ta wallafa.

Rahotanni sun ce wata tawagar gwmanatin, karkashin jagorancin ministan ciniki na kasar ta Sudan Hatim al-Sir, sun ziyarci jihar White Nile mai makwabtaka da Sudan ta kudun a ranar Litinin domin sake bude cigaba da huldar cinikayya tsakanin kasashen biyu.

An ruwaito ministan da cewa, wannan mataki zai takaita fasa-kwaurin kayayyaki tsakanin bangarorin biyu.

Ministan ya bukaci a samar da wani tsari na bai daya wanda zai sake farfado da harkokin cinikayya a kan iyakokin kasashen biyu.

A ranar 15 ga watan Afrilun shekarar 2014, kasar Sudan ta yanke shawarar dakatar da huldar cinikayya a kan iyakarta da Sudan ta kudu, wadda ke fama da yakin basasa tun a shekarar 2013.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China