in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin Sin zai bada gudumowar kayayyakin wasanni a makarantun kasar Sudan 50
2018-02-10 13:39:30 cri

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Khartoum ya sanya hannu kan yarjejeniyar tallafawa gidauniyar Sanad, inda zai bayar da gudumowar kayayyakin wasannin motsa jiki ga makarantu 50 a kasar Sudan.

A yayin bikin, Samia Mohamed Osman, darakta janar ta gidauniyar ta Sanad, ta yabawa yarjejeniyar da aka kulla tsakanin gidauniyar da ofishin jakadancin kasar Sin dake Khartoum, tana mai cewa, sama da shekaru biyar ke nan da aka kulla yarjejeniyar a bangarorin samar da tufafin da ake sawa a lokacin hunturu, da ayyukan samar da lantarki ta hanyar amfani da hasken rana, da samar da kayayyakin kiwon lafiya masu yawa a kasar.

A nasa bangaren, Jakadan kasar Sin a Sudan Li Lianhe, ya yabawa dangantakar dake tsakanin Sin da Sudan, wanda ya bayyana ta da cewa mai dadadden tarihi ce, kana an samu zurfafa mu'amala tsakanin kasashen biyu a fannoni masu yawa.

Jakadan na Sin ya nanata aniyar kasarsa na cigaba da karfafa mu'amalarta da Sudan domin cin moriyar kasashen biyu, ya kara da cewa, kasar Sin na cigaba da ayyukan tallafawa bangaren ilmin kasar ta Sudan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China